Sakataren gwamnatin Nijeriya Sanata George Akume ya ce manyan 'yan siyasar Arewacin Nijeriya su yi hakuri har sai Shugaba Tinubu ya kammala wa'adi na biyu na mulkin kasar kafin su fara nema.
Ya ma kama sunan Atiku Abubakar, inda ya ce, daina tunanin zai zama shugaban kasa a 2027.
George Akume wanda ya yi magana a cikin shirin siyasa na gidan talabijin na TVC kamar yadda jaridar Daily Trust ta wallafa, ya ce Kudancin Nijeriya ne ke da alhakin samar da shugaban kasa a shekarar 2027.
Ya ma yi nasiha ga Atiku Abubakar na PDP cewa idan Allah Ya so zai zamo shugaban kasa, ko ya shekara 90 a duniya zai iya zama.
Category
Labarai