Tsohon ministan matasa da harkokin wasanni Solomon Dalung, ya bayyana yadda masu hana ruwa gudu su ka yi baba-kere tare da ƙwace iko bayan nasarar da shugaban kasa Muhammad Buhari ya samu a shekarar 2015.
Da yake magantawa a cikin wani shiri da aka yada a ranar Lahadi, Dalung ya ce wadannan mutanen na daga cikin wadanda ya baiwa mukamai domin su taimaka masa sai dai sun yi amfani da damar wajen ci gaban kansu.
Solomon ya soki yadda mutanen da suka taimakawa Buhari wurin cin zaɓe su ka tafi wurin murna su ka bar shi da 'yan hana ruwa gudu.
Category
Labarai