Janar Olufemi Oluyede, shugaban sojoji na kasa a Nijeriya |
A dukkanin ayyukanmu muna sanya tsanaki da bin ka’idoji kafin mu jefa bama-bamai ko wani abu makamancin hakan. Wannan shi ne babban sakon da ke cikin sanarwar ta rundunar hadin giwa ta Operation Fansar Yamma.
Jaridar The Nation ta ruwaito rundunar na cewa jami’anta sun tattara bayanai tare da samun tabbaci kafin sakin bama-bamai a kan Lakurawa a kauyukan Gidan Sama da Rumtuwa na karamar hukumar Silame ta jihar Sokoto.
Ta kara da cewa zargin cewa jirgin saman sojoji ya kai hari a gidajen al'umma tare da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, abu ne da ya kamata kafafen yada labarai da sauran jama’a su nemi sahihancinsa daga majiyoyi masu tushe.
A wata sanarwar da Kodinetan yada labarai na rundunar Fansan Yamma da ke yaki da 'yan ta'adda a jihohin arewa maso yammacin Nijeriya Laftanal Kanar Abubakar Abdullahi ya fitar a ranar Laraba da daddare, ya ce rundunar na daukar dukkanin matakan da suka dace kafin kai hari ga 'yan ta'adda domin tabbatar da cewa bai shafi fararen hula ba.
Sanarwar ta yi gargadin cewa, akwai barazanar yin amfani da labarai da ba su da inganci wajen yi wa rundunar bakin fenti, dangane da yakin da take yi da 'yan ta'adda, a don haka ta bukaci al'umma da su daina yadda da jita-jita na labarin da ba shi da tushe, tana mai cewa idan ba a yi taka-tsantsan ba, ‘yan ta’adda za su iya amfani da irin wannan dama wajen yada labaran bogi.
Sanawar da sojojin suka fitar na zuwa ne ‘yan sa’o’I bayan da shugaban karamar hukumar Alhaji Abubakar Muhammad Daftarana ya ce sojoji sun yi wannan hari bisa kuskure, kuma a sanadin haka mutane akala 10 ne suka rasu.
Haka zalika gwamnan jihar Sokoto Dr Ahmad Aliyu ya halarci jana'izar mutanen tare da baiwa al'ummar kauyukkan Gidan Sama da Rumtuwa tabbacin bin kadin lamarin domin yin binciken yadda lamarin ya faru.
DCL Hausa
Ukashatu Ibrahim Wakili