Marcus Rashford |
Dan wasan gaba na Manchester United Marcus Rashford na nemarwa kansa mafita bayan ya gaza birge mai horaswarsa Ruben Amorin daidai lokacin da kungiyar ta nuna alamun raba gari da shi muddun bai kara himma ba.
Jaridar wasanni Sky Sport ta rawaito Dan wasan mai shekaru 27 na takun saka da mahukuntan United bayan rashin jituwa da ya rinka samu da tsohon mai horaswarsa Erik ten Hag.
Sai dai har yanzu Rashford ya kasa yin abin kirki lamarin da ya sanya aka benca shi a karawar da United ta yi da City a karshen mako.