Yan wasan Tottenham da Man United |
Kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta kai wasan kusa da karshe a gasar EFL Cup bayan doke Manchester United da ci 4 da 3 a daren Alhamis.
United karkashin jagorancin Amorim ta gaza kai wa wasan kusa da karshe a gasar bayan rashin nasarar da ta yi har magoya bayan kungiyar suka nuna bacin ransu.
Yanzu haka kungiyoyi hudu sun kai zagayen na Semi Final a gasar ta EFL Cup ta kasar Ingila ta shekarar 2024.
Kungiyoyin da suka kai zagayen na kusa da karshe sun hada da, Arsenal, Liverpool, Newcastle da kuma Tottenham Hotspur.