Majalisar wakilan Nijeriya ta dage yin muhawara akan dokar garambawul ga haraji da ta shirya gudanarwa a ranar Talata, biyo bayan matsin lamba daga gwamnoni 19 na arewacin kasar.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa, dakatarwar na kunshe a cikin wani sako da akawun majalisar Dr Yahaya Danzaria, ya aikewa 'yan majalisar mai dauke da kwanan watan 30 ga watan Nuwamban 2024.
Daga cikin wadanda ke adawa da wannan kudurin dokar akwai 'yan majalisa 48 daga arewa yankin arewa maso gabas, sai 'yan majalisa 24 na jihar Kano da kuma tsohon gwamnan jihar Sokoto Sanata Aminu Waziri Tambuwal.