Majalisar dokokin Nasarawa ta rage kasafin kudin 2025
Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta zaftare kasafin kudin shekarar 2025 da aka amince da shi a baya daga Naira biliyan 402 da miliyan 500 zuwa Naira biliyan 384 miliyan 300.
Kakakin majalisar, Danladi Jatau, shi ne ya sanar kwaskwarima a kasafin kudin, a wani zaman gaggawa da majalisar ta yi ranar Juma'a a garin Lafiya babban birnin jihar.
Jatau, ya kuma ce rage kasafin ya biyo bayan shawarar da majalisar zartarwar jihar ta bayar, cewa kasafin kudin da aka yi a baya ya haura kudaden shigar da jihar ke samu.