Majalisar dokokin Jihar Kano ta yi watsi da kudirin gyaran haraji


Majalisar dokokin jihar Kano ta yi fatali da kudirin gyaran haraji da yanzu haka majalisun dokokin Nijeriya ke aiki a kai.

A zaman majalisar Kanon na ranar Litinin, karkashin jagorancin Ismail Falgore, 'yan majalisar sun nuna kin amincewa da kudurin bayan tattaunawa a zauren.

A wani kudurin gaggawa da shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Husseini ya gabatar, ya ce akwai bukatar dukkan 'yan majalisar yankin arewacin kasar su yi duk mai yiwuwa don ganin kudurin bai yi nasara ba, yana mai cewa babu ta yadda zai amfanar da al'ummar arewa.

Majalisar ta kuma yi kira ga ‘yan majalisar dattawa da na wakilai musamman ‘yan yankin arewa da su gaggauta hana zartar da kudirin.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp