Majalisar dokokin jihar Adamawa ta amince da wata doka da za ta bada damar kirkiro da ƙarin masarautu masu daraja ta daya a jihar.
Dokar wadda ke jiran Gwamna Ahmadu Fintiri ya sanya mata hannu domin tabbatar da ita, na zuwa ne kwanaki kadan bayan da gwamnan ya sanya hannu kan dokar da ta kirkiro da gundmomi 83.
Sabuwar dokar za ta sauke Lamidon Adamawa, Mustapha Barkindo, daga zama shugaban majalisar sarakuna na din-din-din, muƙamin zai zama wa'adin shekara 1 tsakanin sarakunan.