Majalisar dattawan Najeriya ta yi alkawarin yin duk mai yiwuwa don samar da makamashi mai dorewa


Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce majalisar dokokin Nijeriya za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau don zuba jari a ayyukan samar da makamashi mai dorewa. 

Akpabio ya bayyana haka ne yayin wani taron bunkasa samar da makamashi wanda rukunin kamfanonin Solewant suka shirya a Jihar Rivers, mai taken, “bai wa fasaha da ƙirƙira fifiko don samar da makamashi mai dorewa a Afirka”

Shugaban majalisar dattawan wanda mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Osita Ngwu ya wakilta, ya ce za su yi duk abin da ya kamata wajen tallafawa ‘yan kasuwa na cikin gida domin su amfana da tsare-tsaren samar da ingantaccen makamashi ta hanyar fasahar kere-kere.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp