Majalisar dattawan Nijeriya ta kafa wani kwamiti da zai yi aiki kan korafe korafen da ake yi kan kudurin dokar haraji da ya janyo cece-kuce a kasar.
Mataimakin shugaban majalisar Sanata Barau Jibrin ne ya sanarda hakan a zaman majalisar na yau.
Kwamitin karkashin jagoranci shugaban marasa rinjaye Sanata Abba Moro zai yi aikin gyara duk wani bangare da ake korafi akai tare da hadin gwuiwar ofishin babban lauya na kasa da kuma duk bangarorin da ke da ruwa da tsaki.