Ma'aikatan gwamnatin Nijeriya na sun fara shagulgulan buki Kirsimeti a wani yanayi na Allah Ka wadata mu, saboda tsaikon biyan albashin watan Disamban 2025.
Binciken jaridar Punch ya nuna cewa ko albashin watan Nuwamba wasu ma'aikatan ba su sake shi ba sai a mako na biyu na watan Disamba, abinda da dama daga cikin ma'aikatan ke kokawa.
Wasu majiyoyi sun ce matsalar ta faru ne a ofishin akanta na kasa yayinda wasu su ka alakanta tsaikon da aka samu da sauyin tsarin biyan albashin da aka yi da wata sabuwar manhaja.