Ma'aikatan banki a Nijeriya sun zargi CBN da kara ta'azzara rashin takardun kudi a kasar

Kungiyar manyan ma’aikatan bankuna da na kamfanonin Inshora da sauran cibiyoyin kudi ta Nijeriya ta zargi babban bankin kasa CBN da gazawa wajen samarwa da bankunan kasuwanci kudaden da ake bukata.

Shugaban kungiyar Olusoji Oluwole, ne ya bayyana hakan a wata hira da jaridar PUNCH, inda ya haska irin illar da karancin takardun kidin ke haifarwa, musamman ganin yadda lokacin bukukuwa Kirsimeti da sabuwar shekara ke kara gabatowa. 

 A cewar, Oluwole, bankunan suna da manyan hanyoyin samun kudi guda biyu ne kawai ta farko daga CBN ta biyu kuma daga dillalai, sai dai ya ce babban bankin ya gaza samar da kudaden da bankuna ke bukata.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp