Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta sanar cewa sabuwar kungiyar 'yan ta'addar nan ta Lakurawa ne ke da alhakin tayar da abin fashewa a kauyukan yankin Dansadau cikin karamar hukumar Maru ta jihar.
Jaridar Daily Trust ta ce, kwamishinan 'yan sandan jihar CP Muhammad Shehu Dalijan ne ya sanar da hakan a zantawarsu ta wayar salula.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin a kauyen 'Ya Tasha, CP Dalijan ya ce mutum daya ne kawai ya mutu, uku suka samu raunuka.