Kungiyar Wolves ta nada Vitor Pereira a matsayin sabon mai haras da ita

Wolves ta nada Vitor Pereira a matsayin sabon kocinta

Kungiyar Kwallon kafa ta Wolves ta sanar da nada Vitor Pereira a matsayin sabon mai horar da ita.

Dan kasar Portugal ya koma Wolves ne daga Al-Shabab ta Saudiyya kan kwantaragin watanni 18, da zabin kari idan har ya taka rawar gani.

Pereira ya maye gurbin Gary O'Neil wanda aka kora a ranar Lahadi bayan rashin nasarar da ya yi ranar Asabar a hannun Ipswich da ci 2 da 1.

A ranar Alhamis ne Pereira ya fara jan ragamar kungiyar karon farko a filin atisaye kuma zai fara wasa ne da Leicester City da ke matsayi na 17 a teburin gasar Premier league ta Ingila, wadda ke da banbancin maki biyar tsakaninta da Wolves.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp