Kungiyar ECOWAS ta matsa kaimi domin samar da kudin bai daya ga mambobin ta
Kungiyar ci gaban kasashen yammacin Afrika ECOWAS ko kuma CEDEAO, na ci gaba shirye-shirye kaddamar da kudin bai daya a yankin mai suna ECO, biyo bayan cimma matsayar da aka yi a yayin taron kasashen karo na 65.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwar karshen taron da shugabannin kasashen suka gudanar karo na 66 a tarayyar Nijeriya Abuja.
A baya dai kungiyar ECOWAS dake da kasashe 15, ta shirya kaddamar da kudin ECK a shekarar 2020, amma cutar korona ta kawo tsaiko inda a halin yanzu aka sanya 2027 a matsayin ranar kaddamarwa.
Hukumar ta ce ta yi amfani da shawararin da babban kwamiti ya gabatar, na zabar kasashe da za a kaddamar da tsarin da kuma wadanda za su shigo daga baya.