Kungiyar direbobi masu dakon kaya ta Nijeriya ta koka kan karbar haraji ba bisa ka'ida ba a jihar Kogi

Kungiyar direbobi masu dakon kaya ta Najeriya HDHTAN reshen jihar Kogi, ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta ba da goyon baya don kawo karshen karbar haraji daga mambobinta ba bisa ka'idaba. 

Shugaban kungiyar ta HDHTAN reshen jihar Kogi, Trust Chukwuma, ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin taron manema labarai da ya kira a Lokoja, inda ya bayyana nasarorin da kungiyar ta samu daga kafuwarta, da suka hada hana aikata miyagun ayyuka ta hanyar amfani da manyan motoci. 

Ya kuma ce wannan kokarin ya taimaka wajen sanya ido kan yadda ake amfani da manyan motoci ana aikata miyagun laufuka, da kuma bada rahoton laifukan ta’addanci, kamar garkuwa da mutane, da safarar mutane.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp