Femi Adesina |
Tsohon mai ba tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama'a, Femi Adesina, ya bayyana ubangidan na shi a matsayin masoyin talaka.
Adesina ya ce irin wannan la’akari ne ya sa ya yanke shawarar kin cire tallafin man fetur a matsayinsa na shugaban Najeriya.
Femi Adesina ya bayyana hakan ne a wani taron karramawa da aka yi wa Buhari wanda ya cika shekaru 82 a duniya.
Category
Labarai