Kudirin kasafin kudin 2025 ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa


Majalisar dattawan Nijeriya ta amince kudurin kasafin kudin 2025 da ya kai tiriliyan 49.7 ya tsallake karatu na biyu, bayan da shugaban kasa Bola Tinibu ya gabatar da shi a ban majalisun kasar.

Amincewar na zuwa ne, yayin da majalisar ta tafi hutu har zuwa 14 ga watan Janairun 2025 domin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara.

Yayin zaman majalisar na yau Alhamis, 'yan majalisar sun tafka muhawara kan kasafin kudin wanda ya baiwa bangaren tsaro fifiko.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp