Kotun kolin Nijeriya ta yi watsi da karar da aka shigar kan Shugaba Bola Tinubu akan zarge-zargen tu'ammali da miyagun kwayoyi da kuma binciken hukumar leken asiri ta Amurka CIA.
Karar wadda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar HDP a shekara ta 2019 Ambrose Aworu ya shigar, ya nemi kotu ta sauke Shugaba Tinubu.
Sai dai a hukuncin kotun mai alkalai biyar, karkashin jagorancin Mai Shari'a Uwani Abba-Aji, ta yi watsi da karar da tace ba ta da tushe kuma ta ci tarar Ambrose Aworu naira miliyan 5. Hakama ta umurci akawun kotun kar ya koma karbar irin wannan karar daga wanda ya shigar da ita Ambrose Aworu.
Category
Labarai