Yahaya Bello |
Babbar kotun tarayya da ke Maitama a babban birnin Nijeriya Abuja, ta yi watsi da bukatar bayar da belin tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello.
Da ta ke yanke hukunci a zaman kotun na ranar Talata mai shari’a Maryanne Anenih, ta yi zargin rashin cancantar neman belin na Yahaya Bello.
Tun da farko, hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta Nijeriya EFCC ce, ta gurfanar da Yahaya Bello, tare da wasu mutane biyu a gaban kotun, bisa tuhumar su da karkatar da makudan kudade da yawansu ya kai Naira biliyan 110.
Category
Labarai