![]() |
Kotu ta yanke wa masu garkuwa da mutane hukuncin kisa |
Wata babbar kotu a Jihar Jigawa ta yanke wa wasu masu garkuwa da mutane hukunci kisa ta hanyar rataya.
Da ya ke zartar da hukunci alkalin kotun mai shari’a Mohammed Musa Kaugama ya ce an sami mutanen biyu da laifuka bakwai da suka hada da yin garkuwa da mutune da hada baki da fashi da makami da haura gidan mutane.
A ranar 21 ga watan Yunin 2021 ne mutanen biyu wato Sani Mohammed da Babannan Saleh, dauke da makami suka haura gidan Hamidi Abdu da ke garin Shangel a karamar Hukumar Ringim inda suka kwace masa kudade masu yawa sannan suka ta fi da shi, daga baya suka nemi kudin fansa har naira miliyan 12 kafin su sake shi.