Kotu ta rufe wata coci a Lagos bisa zargin damfara

Wata babbar kotun jihar Lagos da ke zaune a Ikeja, ta yanke wa wasu ma’aurata, Harry Uyanwanne da Oluwakemi Odemuyiwa, hukuncin daurin shekaru 16 a gidan yari tare kuma soke rijitar majami'ar Temple International. 

Mai shari’a Mojisola Dada ta yanke hukuncin ne bayan ta same su da laifukan da ake tuhumarsu.

Tun da farko dai hukumar EFCC ce ta gurfanar da su a gaban kotu, inda take tuhumarsu, da amfani da majami'ar wajen damfarar mutane, tare da yi musu zambo cikin aminci.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp