Wata babbar kotu a jihar Kano ta dage saurararen karar da aka shigar da tsohon gwamnan jihar Dr Abdullahi Ganduje kuma shugaban jam'iyyar APC tare da wasu mutane bakwai har sai zuwa ranar 13 ga watan Fabrairu 2025.
Karar wadda gwamnatin jihar Kano ta shigar, ta ƙunshi tuhume-tuhume na cin hanci, wadaka da dukiyar al'umma da kuma karkatar da biliyoyin naira da take yi wa Ganduje, da matarsa Hafsat Umar da wasu mutum 6.
A zaman kotun na yau Laraba, ta saurari bangaren wadanda ake kara inda ta dage zamanta har zuwa shekara mai zuwa.