Fasfo |
Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya NIS da ta biya Benita Ezumezu diyyar Naira miliyan 3 sakamakon gaza ba ta fasfo din ta cikin makonni shida da aka kayyade.
Kotun ta kuma umarci Olubunmi Tunji-Ojo, ministan harkokin cikin gida, da hukumar ta NIS, su tabbatar da cewa wadanda suka cika dukkan sharudda an basu fasfon su cikin makonni shida kamar yadda doka ta 9(4) ta dokar hukumar shige da fice ta shekarar 2015 ta tanada.
Alkalin kotun, Mai shari’a Emeka Nwite, ya bayar da umarnin ne a lokacin da yake yanke hukunci a wata kara mai lamba FHC/ABJ/CS/75 da Benita Ezumezu ta shigar, sakamakon bata ma ta lokaci da aka yi har tsawon wasu watanni kafin ta samu fasfo dinta, wanda ta nema a watan Oktoban 2022.