Kotu ta ce gwamnatin Kano ta biya diyyar rusau biliyan 8.5


Wata kotu a jihar Kano ta tilastawa gwamnatin jihar biyan diyya har biliyan N8,511,000,000 ga wani kamfani Lamash Properties Limited da gwamnatin karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta rushewa gine-gine.

Kotun ta kuma umurci wadanda ake kara da su biya su biya karin naira miliyan 10, diyyar kudaden da kamfanin ya kashe wurin shigar da kara.

Kamfanin Lamash Properties Limited ya shigar da karar ne yana zargin gwamnan da rusa gine-ginen ba bisa ka'ida ba a shekara ta 2023.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp