Kotu ta baiwa hukumar yaki da cin hanci a Nijeriya EFCC, damar rufe asusun bankuna 67 bisa zargin zambar kudade miliyan 52.9


Wata babbar kotun tarayya ta baiwa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya EFCC damar garkame asusun bankuna 67 bisa zargin zambar kudade da suka kai miliyan 52.9.

Mai Shari'a Emeka Nwite ne ya yi hukuncin bayan da lauyan hukumar EFCC, Martha Babatunde, ta shigar da takardar neman izini.

Takardar neman izinin wadda aka gabatar, ya neman a bai wa shugaban hukumar ko wani jami'in EFCC damar baiwa daraktocin bankuna umurnin rufe asusun da ake bincike a kansa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp