Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, ta bayar da umarnin a cigaba da rike wasu makudan kudade da aka kwace har dalar Amurka 49,600 a hannun tsohon Kwamishinan Zaben jihar Sokoto a zaben da ya gabata na 2023.
Mai shari’a Emeka Nwite ya ba da umarnin ne bayan da lauyan hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC, Osuobeni Akponimisingha ya gabatar da bukatar.
Category
Labarai