Kungiyar kiristocin Nijeriya ta bukaci Tinubu ya rage farashin kayan abinci |
Kungiyar kiristocin Nijeriya CAN ta bukaci gwamnatin tarayya da ta karfafa bangaren aikin gona da kuma rage farashin kayan abinci tare kuma da samar da daidaito a tsakanin yan kasa.
Shugaba Kungiyar Archbishop Daniel Okoh, ne ya mika wannan bukata a sakonsa na Kirsimeti ga mabiya addinin kirista, inda ya bukaci kiristoci da su rubanya riko da koyarwar Yesu domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al'umma musamman a irin wannan lokaci na tsanani.
Ya kuma nuna alhininsa game da yadda bikin na bana ya zo da wani irin yanayi na tausayi, musamman ganin yadda mutane suka rasa rayukansu a turmutsitsin karbar sadaka da ya gudana a Abuja da Ibadan da kuma Anambra.