Kingibe ta fice daga majalisa a fusace bayan da Akpabio ya dakatar da kudirinta game da rusau a Abuja

Akpabio da Kingibe 

Wani lamari mai kama da almara ya faru a zauren majalisar dattawan Nijeriya a ranar Alhamis lokacin da Sanata Ireti Kingibe, mai wakiltar Abuja babban birnin kasar ta fice a fusace bayan an hana ta gabatar da wani kudiri game da rasau a birnin tarayyar. 

Lamarin ya faru ne yayin zaman majalisar, wanda aka yi ta gabatar da batutuwa ba tare da matsala ba, har sai da shugaban majalisar Godswill Akpabio, ya hana Sanatar damar gabatar da kudirin. 

Wannan batu dai, ya haifar da yamutsa hazo a tsakanin Sanatocin har ta kai ga Sanata Kingibe ta fice daga zauren majalisar baki daya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp