Kashi 70 cikin 100 na ‘yan Najeriya sun ƙi karbar tayin karbar cin hanci a shekarar 2023 - ICPC


Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta ta Nijeriya ICPC, Musa Adamu Aliyu (SAN) ya ce Kashi 70 cikin 100 na ‘yan Nijeriya da aka yi wa tayin karbar cin hanci a shekarar 2023 sun ƙi karba.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ke neman hadin haɗin kan sauran hukumomi wajen yaki da cin hanci da rashawa, ganin cewa babu wata hukuma guda da za ta iya wannan aiki ita kadai. 

Shugaban hukumar ta ICPC ya bayyana hakan ne yayin wani taro da ya gudana a jihar Kano kan karfafa aikin hukumar na dakile cin hanci da rashawa. 

Taron wanda babbar manufarsa ita ce samar da hadin gwiwa wajen yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya. 

Ya ce, babu wani bangare na gwamnati ko matakin gwamnati ko hukuma da zai iya yaki da cin hanci da rashawa don haka akwai bukatar samun hadin kai don ganin an kai ga gaci.

Yayin taron babbar Jojin jihar Kano, Mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ta yaba da yadda hukumar ta ICPC ke bibiyar matakan da suka dace wajen yaki da cin hanci da rashawa. 

Ta ce aiwatar da doka da kuma gurfanar da wadanda ake zargi wajibi ne, amma yin kan da garki dabara ce, wadda ke magance tushen cin hanci da rashawa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp