Kasar Belgium ta amince da wata doka da zata baiwa karuwai 'yanci da kuma kariya kamar sauran ma'aikatan kasar.
Dokar wadda aka sanyawa hannu jiya Lahadi, za ta tabbatar da cewa an baiwa karuwai hutun haihuwa da fansho da kuma kare su daga cin zarafi.
Wannan na zuwa ne bayan gagarumar zanga-zangar da ta faru a shekara ta 2022 lokacin annobar korona, inda masu aikin karuwanci su ka bukaci gwamnati ta kare sana'arsu tare da basu tallafi.