Rahoton Khadija Nasidi, Kano
Al’umma da dama a sassan Nijeriya, musamman mata kananan yara, na fuskantar cin zarafi ta hanyoyi daban-daban. Hakan wasu na ganin ya zama ruwan dare a lungu da sako na kasar.
Alkaluma na baya-bayan nan Kamar yadda ministan Mata a Nijeriya ta shaida wa jaridar Punch sun nuna cewa kusan kashi 30% na mata a Nijeriya sun fuskanci wani nau’i na cin zarafi. Ko da yake ba kamar a shekarun baya ba, za a iya cewa yanzu an samu ci gaba wajen dakile wannan damuwa.
Ko da yake duk da wadannan alkaluma, gwamnatin Nijeriya tare da daidaikun mutane da kungiyoyi sun ce suna daukar muhimman matakai na yaki da cin zarafin mata da kananan yara. Akwai dokoki da aka tanada game da cin zarafi da bayar da kariya ga wadanda suka tsira da kuma hukunta masu laifi. Kamar yadda dokar kare hakkin yara ta 2003 ta nuna.
Malama Halima Adamu (mun sakaya sunanta) wadda ta kubuta daga hannun mijinta da ya kwashe shekaru yana cin zarafinta ta ce akwai lokacin da sai da ta kusa kashe kanta saboda bugun da mijinta ya ke yi mata.
Halima ta ce ta fara fuskantar cin zarafi ne tun farkon aurenta dalilin iyayenta sun kasa cika mata gidan da ya kama su zauna da kayayyaki, inda ya ce ya kama gida mai sashe biyu inda ita kuma iyayenta suka sa mata kaya a sashe daya daidai karfin su tare da barin dayan sashen don mijin ya sa kaya ganin cewa sashensa ne.
Ta ce “Miji na ya fara mari na ne saboda na yi shiru ban tanka shi ba a lokacin da yake min fada, wai hakan na raina shi kenan.”
“Tun daga wannan mari na farko na zama kamar jaka, duk sanda ranshi ya baci to kuwa a kai na yake hucewa ko da kuwa ba ni na bata masa rai ba.”
Sai dai duk da haka ganin yadda ba ta taba kai kara ba, ta rika boye halin da take ciki, kuma tana kyautata zaton mijin nata zai daina bugunta tunda a duk lokacin da ya buge ta daga baya yana dawowa ya bata hakuri amma a kwana a tashi abu sai kara girmama yake har ta kai matsayin da Halima tana fita cikin hayyacinta ko kuma tana waje amma kamar bata nan.
“Wani lokaci da ya fusata ya hau ruwan ciki na ya min bugun tsiya lokacin da nake da ciki, wanda a wannan bugun ne ya lahanta jaririn ciki na da ya kai wata shida, daga baya na rasa cikin. Wannan kuma ba shi ne ciki na farko da nake rasawa ba saboda bugun da miji na yake min.”
Saboda tsananin damuwa akwai ranar da Halima ta dauki wuka da niyyar ta kashe kanta ta huta amma sai tunanin ‘ya’yanta da ba su da alhakin kowa ya hana ta.
Dama dai Halima tana zuwa makaranta tunda aka yi mata aure, amma sai dai ba ta samun sararin yin karatu da har za ta ci jarrabawa saboda halin da take ciki a gidan aurenta.
Wane mataki hukumomi ke dauka?
Gwamnatin Nijeriya ta yi kokarin ganin an aiwatar da dokokin da za su kare hakkin wadanda lamarin ya shafa inda jihohi daban-daban suka kafa rundunan aiki don magance cin zarafin mata yadda ya kamata.
Bugu da kari, an kaddamar da gangamin wayar da kan al'umma, da ilmantar da jama'a game da 'yancin mata. kungiyoyin kare hakkin mata kamar kungiyar CITAD mai yaki da nuna wariyar jinsi a cibiyar bunkasa fasaha ta sadarwa da ci gaban al’umma sun ba da muhimmiyar gudunmuwa wajen ba da agajin shari’a da tallafa wa waɗanda suka tsira ta hanyar dogaro da kai.
A cewar Malama Zainab Aminu jami’ar yaki da nuna wariyar jinsi a cibiyar bunkasa fasaha ta sadarwa da ci gaban al’umma a jihar Kano, ana cin zarafin mata da maza da yara kanana amma sai dai an fi cin zarafin mata da kananan yara.
Malama Zainab Aminu ta ce bincikensu, ya gano cewa a duk fadin Nijeriya jihar Kano ce ta fi kowace jiha, rahoton cin zarafin mata da kananan yara. Saboda haka ne suka dukufa domin ganin an kawo karshen wannan matsala.
Malama Zainab ta ce suna fadakarwa a shafukan sada zumunta tare da ba malamai da iyayen kasa shawarar fadakar da mata kan 'yancinsu, da kuma yadda za su fito su bayyana cewa ana cin zarafinsu.
Hakika al’umma na tashi daga baccin da suke yi domin kuwa kungiyarsu na samun hadin kai wajen dakile wannan matsala. Sai dai ya kamata mutane su rika kai rahoton cin zarafi ga hukumomi domin hukunta wanda ya aikata laifin, ba sani ba sabo.” In ji Malama Zainab.
Sai dai duk da wannan ci gaba, akwai kalubale, duba da yanayin al'ada wadda ke sa a kyamaci ko a guji wanda abin ya shafa, ko kuma ma a kasa bi wa wadda abin ya shafa hakkinta a shari’ance, wannan ke hana mata da dama bayyana halin da suke ciki. Don haka yana da muhimmanci a cike wannan gibi don tabbatar da an kawo karshen wannan matsala a cewar Malama Zainab.
Duk da cewa Nijeriya ta samu ci gaba a fagen yaki da cin zarafin mata da 'yan mata, akwai buƙatar karin haɗin kai daga gwamnati, al'ummomi, da daidaikun mutane don tabbatar da cewa kowace mace za ta iya rayuwa ba tare da fargabar wani zai ci zarafinta ba a gida ko a waje kai koma a dokar daji ne.
Wani rahoton asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF na shekarar 2024, ya gano yadda a cikin duk mintuna 4, ana samun yaron da aka kashe a sashen duniya. Kazalika, kusan yara milyan 90 da ke doron duniya yanzu haka, an ci zarafinsu ta hanyar keta musu haddi. Bugu da kari, akwai 'yan mata wato masu matsakaitan shekaru (tsakanin shekara 15-19) kusan milyan 50 da aka keta wa haddi a duniya.
Sai dai wani wani rahoton asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ya ce 6 cikin 10 na yara sun taba fuskantar wani nau’i na cin zarafi a Nijeriya. Sannan kuma daya a cikin yara mata 4 sun taba fuskantar fyade a kasar. Duk da dai rahoton bai bayyana jihohin da lamarin ya fi kamari ba, amma kusan kowane lungu da sako na Nijeriya ana samun wannan matsala kamar yadda binciken rahoton ya gano.
*Yadda Halima ta kubuta daga cin zarafin da mijinta ke yi mata*
Har tsawon wani lokaci Halima ta ci gaba da fuskantar wannan cin zarafi daga mijinta, sai watarana ta ji 'yarta tana fadin cewa ‘’dama mota ta kade Abbana ya mutu ko Ummata za ta huta da bugun da yake yi mata.
Hankalin Halima ya yi matukar tashi da ta ji wannan magana da 'yarta ta yi, tun a wannan lokacin ta kudiri aniyar rabuwa dashi har watarana ta hadu da wata a makaranta ta ba ta labarin halin da take ciki wanda wannan matar ce ta hada ta da wata malamar kula da dabi’ar dan'adam.
Malama Farida dai ta fara da jin ta bakin Halima ta kuma fuskanci cewa matsalar mijinta babba ce don haka ta fara da saka ta wani rukuni da take ba da darasi ga mata da ke cikin damuwa a manhajar Whatsapp. Sannu a hankali Halima ta fara dawowa hayyacinta har ta kai ta nemi saki daga wajen mijinta, sai dai mijin nata ya ki ba ta takarda duk da cewa ta tattara kayanta ta koma gidan iyayenta.
Daga karshe dai kotu ce ta raba auren nasu bayan Halima ta biya shi kudin sadaki.
Kuma kotu ta ba da damar yaranta su rika ziyartarta a duk hutun makaranta da suka yi, wanda mijin nata bai karya wannan doka ba.
*Matsayar Gwamnatin Kano kan cin zarafin mata*
Gwamnatin jihar Kano a kokarinta na ganin an aiwatar da dokokin da za su kare hakkin wadanda lamarin ya shafa ta kafa hukumomi irinsu HISBAH don magance cin zarafin mata yadda ya kamata. Hukumar Hisbah ita ce ke sanya ido kan ayyukan bata gari da kuma gyaran tarbiyya a jihar ta Kano.
Mataimakin kwamandan Hisbah Dr Mujahid Aminudeen ya bayyana cewa hukumar ta Hisbah na taka muhimmiyar rawa wajen kwatowa matan da aka ci zarafi hakkinsu. Da farko dai suna fara tabbatar da lafiyar wanda aka ci zarafi kafin su kai kotu, ya tabbatar da cewa idan suka kai karar kotu suna bibiyar shari’a tare da wasu ma’aikatan tsaro don ganin sun yi nasara wajen hukunta mai laifin.
Dr Mujahid ya kara da cewa hukumar tana kara ba mata da ma mutane baki daya karfin guiwar ba da rahoton cin zarafi a duk inda ya faru domin hakan zai kawo sauki ga aikin su wajen ganin an kawo karshen abin.
Matamakin kwamanda ya yi kira ga mata da su kara kare kansu tare da takatsantsan kan wadanda za su aminta da su. Ya kuma shawarci maza da su kyautata wa mata kamar yadda musulunci ya tanada.
*Sarakuna iyayen kasa na da gudunmuwar da za su ba da*
Dahiru Ibrahim Kwaru mai unguwar gidan sarki da ke jihar Kano ya bayyana cewa suna ba da hadin kai ga hukumomi wajen kawo karshen cin zarafin mata. Ya kuma yi kira ga sarakuna 'yan'uwa sa da su samar da zauren sulhu tare da daukar cikakken hukunci akan duk wani mai laifin cin zarafi duk girma sa, duk halinsa, ba sani ba sabo.