John Dramani Mahama |
Hukumar zaben kasar Ghana ta ayyana tsohon shugaban kasar kuma jagoran adawa John Dramani Mahama, a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na ranar Assabar.
Tuni mataimakin shugaban kasar kuma ɗan takarar jam'iyya mai mulki Mahamudu Bawumia, ya amince da shan kaye a zaben.
Hukumar zaben ta ce ta kirga kuri'un mazabun 'yan majalisa 267 daga cikin 276 na kasar, kuma Ya lashe kashi 56.55 na kuri'un.
Category
Ketare