Rahotanni na nuna cewa mutane da dama sun rasa rayukansu yayinda wasu su ka jikkata yayin da wani jirgin sojin saman Nijeriya da ke farautar Lakurawa ya jefa gama bamai ga mutanen wasu kauyukka biyu a karamar hukumar Silamen jihar Sokoto.
Lamarin ya faru ne a ƙauyukan Gidan Sama da Rumtuwa da safiyar yau Laraba, kamar yadda al'ummar yankin su ka shaidawa jaridar Dailytrust.
Wani mai suna Malam Yahaya, ya ce abin ya faru ne a ƙauyukan wadanda ke kusa ga dajin Surame wanda ke zaman wata maboya ta 'yan bindiga da kum Lakurawa.