Jami'an ‘yan sanda sun mamaye gidan Sarkin Kano tare da hana shige da fice a fadar da Sarki Sanusi ke zaune.
Wannan na zuwa ne a yayin da wasu rahotanni ke cewa, Sarki Sanusi Lamido zai yi jawabi ga wasu masana tattalin arziki kan dokar haraji, kamar yadda jaridar Dailytrust ta ruwaito.
Wasu bayanai kuma na alakanta zuwan jami'an tsaron da shirin Sarki Sanusi na rakiyar sabon Wamban Kano, Munir Sanusi zuwa Bichi, inda zai yi hamkimci, a cewar jaridar Dailynigerian
Sai dai jami'an tsaro sun rufe kofar shiga gidan sarkin, tare da harbin iska yayinda 'yan daba suka taru a kofar gidan.
Wasu bayanai na cewa tuni aka Sarki Sanusi ya fita ya bar gidan.
Category
Labarai