Tsohon kakakin majalisa ta 9 ta wakilan Nijeriya Yakubu Dogara, ya alakanta yanayin da yankin arewacin Nijeriya ke ciki na koma baya da shugabannnin yankin.
Ya bukaci 'yan Nijeriya su goyi bayan kudirin Shugaba Buhari na ciyar da kasar gaba ta hanyar dokar garmbawul ga tsarin haraji wadda ke gaban majalisa.
Dogara na jawabi ne a wurin wani taro da shugabannin kiristocin yankin arewacin Nijeriya su ka yi.
Category
Labarai