Sarkin Kano na 16, Muhammad Sanusi na biyu, ya ce a koda yaushe yana fada wa ‘ya’yansa mata cewa idan sun yi aure duk lokacin da mazajensu suka mare su, su mayar da martani.
Ya bayyana haka ne a wajen taron tattaunawa kan yaki da cin zarafin mata ta mahangar addinin Musulunci mai taken: 'Koyarwar musulunci tare da hada kan al'umma don kawo karshen cin zarafin jinsi' daya gudana a Jami'ar Bayero da ke jihar Kano.
Sarkin ya ce, kaso 45 cikin 100 na shari'un da suka shafi cin zarafi a kotunan addinin musulunci na jihar Kano a cikin shekaru biyar, dukkansu dukan Mata ne.
Category
Labarai