Hukumar karɓar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano ta zargi tsohon Manajan Daraktan Kamfanin Samar da Kayan Aikin Gona KASCO, Bala Muhammad Inuwa da karbo umurnin kotu ba bisa ka'ida ba domin mayar masa da kadarorin da hukumar ta kwace a binciken da ta ke yi masa na karkatar da Naira biliyan hudu.
A watan Nuwambar shekarar 2023 hukumar ta gurfanar da tsohon Manajan Daraktan da dansa tare da wasu abokanansa bisa zargin karkatar da naira biliyan 4 daga asusun hukumar ta KASCO zuwa wani asusun ajiya na daban.
A firarsa da gidan talabijin na Channels, sakataren hukumar PCACC Zahraddeen Hamisu Kofar-Mata ya ce sun yi mamakin yadda hukuncin kotun ya je ga rundunar 'yan sanda ba hukumar ba.
Category
Labarai