Hukumar kula da 'yan sandan Nijeriya ta kori jami'ai 19 saboda saba ka'idoji


Hukumar kula da 'yan sanda Nijeriya ta ce ta sallami jami'ai 19 saboda saba ka'idoji da dokokin hukumar.

A yayin zaman majalisar gudanarwa ta hukumar karkashin jagorancin tsohon mataikamin sufeta janar Hashimu Argungu, an ragewa wasu jami'ai 19 mukami saboda aikata laifuka daban-daban.

Wadanda aka sallama sun hada da jami'ai 16 masu mukamin mataimakin sufurtanda, sai manyan sufurtanda 2, da kuma sufustanda 1.

1 Comments

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp