Hukumar karbar korafe-korafe ta kama waɗanda ake zargi da badakalar filaye a Kano ciki har da jami'an tsaro

Hukumar karbar korafe-korafe ta Jihar Kano 

Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta Jihar Kano PCACC, ta kama waɗanda ke da hannu cikin almundahanar filaye, da suka hadar da jami'an tsaro da wasu jami'an gwamnati.

Shugaban hukumar Barrister Muhyi Magaji Rimingado, ne ya sanar da hakan, yayin wani taron tuntuba da hukumar ta gudanar a ranar Talata. 

Rimingado, ya ce an samu nasarar cafke wadanda ake zargin ne bisa aikin hadin gwiwa tsakanin hukumar da jami'an tsaro da ma'aikatar kasa da jami'an ma'aikatar sharia da na kotu, inda ya bayyana kokarin da hukumar ke yi wajen ganin an hukunta duk wanda aka samu da hannu a irin wannan badakala.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp