Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya EFCC ta sanar da kama mutum 792 bisa zarge-zargen zamba a harkar kudaden kiripto da kuma soyayya.
Daraktan hulda da jama'a na rundunar Wilson Uwujaren, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Lagos.
Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a yayin wani gagarumin samame da jami'an hukumar su ka kai maboyar masu aikata zamba, cikin wani gida mai hawa bakwai a unguwar Victoria Island da ke Lagos.
Category
Labarai