Hukumar EFCC a Nijeriya ta samu nasarar karɓe kadara mafi girma tun bayan kafa hukumar zuwa yanzu


Kotu ta sahalewa hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya ta karɓe wani rukunin gidaje 731 dake birnin Abuja, daga wani tsohon ƙusa a cikin gwamnatin tarayya wanda hukumar ba ta bayyana sunansa ba.

Mai Shari'a Justice Jude Onwuegbuzie ne ya bayarda umurnin a cikin hukuncin da ya yanke a yau, a cewar sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook.

Rukunin gidajen dake a yankin Cadastral Zone C09, Gundumar Lokogoma, a Abuja, a yanzu kotu ta hannunta su ga gwamnatin tarayya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp