Hedikwatar tsaron Nijeriya ta karyata wasu rahotanni dake cewa rundunar sojin Faransa na shirin kafa sansani a cikin Nijeriya.
A cikin wani bayani da daraktan yada labarai na hedikwatar Manjo Janar Edward Buba ya ce wannan bayanin ya zama tilas, lura da wasu labarai da ake yadawa cewa, sojojin faransa sun riga sun iso Nijeriya.
Buba ya bukaci al'umma da su yi watsi da wannan labarin da ke ci gaba da karade lungu da sako na kasar.
Category
Labarai