Wani sabon rahoton hukumar kididdiga ta Nijeriya NBS ya ce hauhawar farashin kayayyaki ya karu zuwa kashi 34.60 a cikin watan Nuwamban da ya gabata.
Rahoton ya nuna cewa an samu karin kashi 0.70 a cikin wata daya, inda a watan Oktoba ma'aunin yake a kashi 33.88.
Hakama kididdiga ta shekara daya ta nuna cewa tashin farashin kayan abinci a watan Nuwamba ya kai kashi 38.67, abinda ke nuna ya karu da kashi 11.58 idan aka kwatanta da shekara ta 2023 da tashin farashin kayan abinci yake kashi 27.09.
Category
Labarai