Hasashen Tinubu a kasafin kudin 2025 ba abu ne mai yiyuwa ba - Masani


Wani mai sharhi akan tsare-tsare, Basil Abia ya bayyana cewa hasashen shugaban kasa Bola Tinubu a kasafin kudin shekara ta 2025 ba abu ne mai yiyuwa ba.

A lokacin da ya gabatar da kasafin a zauren majalisar dokokin kasar a jiya Laraba, Shugaba Tinubu ya ce kasafin zai rage hauhawar farashin kayayyaki daga kashi 34.6 zuwa kashi 15 a shekara mai zuwa.

Sai dai a firarsa da Channels TV, Basil Abia ya ce hakan ba abu ne mai yiyuwa ba, ganin cewa har yanzu gangar danyen mai da kasar ke fitarwa bai kai miliyan biyu ba a rana.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp