Hanyoyin kare kai yayin aikin Hajji

1. Ku kasance cikin tsari: Ko yaushe ku rataya katin shaidarku tare da sauraron sanarwa, kuma ku bi umurnin 'yan sanda da sauran jami'an tsaro don tabbatar da tsaro. 2. Takaita shiga cikin taron jama'a: Ku bi hanyoyin da aka kebe da kuma kiyaye lokutan da aka ware muku na zuwa ibada, musamman a lokacin jifan shaidan, don guje wa turmutsitsi, daukewar numfashi sakamakon zafi da kishirruwa. 3. Kishir- ruwa: Ku tabbatar kun sha ruwa sosai tare da kasancewa a inuwa don guje wa matsalolin da ka iya tasowa sakamakon zafin rana. 4. Kiyaye lafiyarku: Kowanne mahajjaci ya kamata ya san wuraren da cibiyoyin lafiya suke, waɗanda ke da wasu magunguna su rinka tafiya ko'ina da su, a rinka yin tsafta, sannan a lura da irin takalman da za a sanya yayin ibada don gudun jin raunuka. 5. Kiyaye ingancin abinci: Ku guji siyan abinci a kan tituna barkatai ko kuma wuraren da ba a tantance tsaftar su ba. 6. Kula da kayayyaki masu daraja: Ku rage yawo da kayayyakinku masu tsada don gudun faduwa ko sacewa. 7. Haramtattun kayayyaki: Haramun ne mahajjaci ya shiga jirgi da duk wani karfe ko wuka ko allura ko reza ko almakashi ko goro ko kuma duk wani nau'in kayan maye.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp