Dr Kwairanga da takwaransa na India |
Kasuwar musayar hannayen jari ta Nijeriya NGX ta bukaci a yi hadin gwiwa tsakaninta da takwararta ta India, tana mai cewa hakan zai tabbatar da dorewar kasuwannin zuba jari a fannin tattalin arzikin duniya.
Shugaban kasuwar ta NGX, Alhaji Umar Kwairanga ne ya bayyana haka a kasar India, yayin wata ziyarar hadin gwiwa da hukumar gudanarwar NGX ta kai kasar.
A cewarsa, duniya na ci gaba da habaka cikin sauri don haka akwai bukatar hada gwiwa da nufin samarwa kasuwannin musayar hannayen jari kyakkyawar makoma.