Gwamnonin Nijeriya sun goyi bayan kafa ‘yan sandan jihohi

Gwamnonin Nijeriya 

Gwamna jihar Kaduna Uba Sani, ya ce jihohi 36 na Nijeriya sun amince da kafa ‘yan sandan jihohi, bayan mika rahotonsu ga majalisar tattalin arzikin kasa.

Gwamnan ya bayyana haka ne a zantawarsa da manema labarai, jim kadan bayan kammala taron majalisar tattalin arzikin kasa karo na 147 wanda mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya jagoranta a Abuja.

Uba Sani ya bayyana cewa jihohi da dama sun amince da kudurin kafa ‘yan sandan jihohi duba da yadda kusan kowace jiha ke fama da kalubalen tsaro. 

Ya kara da cewa hukumomin tsaron da ake da su, ba su da isassun jami’an da za su yi aiki a duka jihohin da kuma kasa baki daya.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp