Ministan wanda ya samu wakilcin Daraktan da ke kula da kwalejojin kimiyya da fasaha a ma'aikatar ilimi ta tarayya, Ejeh Usman, ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin da yake kaddamar da dakunan karatu da na gwaje-gwaje da kayan aikinsu a kwalejin kimiyya da fasaha ta tarayya da ke Bali, a jihar Taraba.
Ya ce gwamnati ta kashe makudan kuɗaɗe har Naira miliyan 390 domin gudanar da aikin, yana mai cewa shakka babu, aikin zai inganta koyo, koyarwa da bincike a kwalejin.